in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ganawa tsakanin shugabannin Sin da Afghanistan
2014-10-28 21:07:43 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Afghanistan Ashraf Ghani Ahmadzai a yau Talata 28 ga wata a nan birnin Beijing, inda Mr. Xi ya jaddada cewa, Sin tana dora muhimmanci sosai kan dangantakar sada zumunci ta hadin kai tsakanin kasashen biyu, kuma Sin na goyon bayan Afghanistan a kokarin da take na mika mulkin kasa cikin lumana da farfado da kasar.

Ban da haka kuma, Mr. Xi ya taya Ashraf Ghani Ahmadzai murnar lashe zaben shugaban kasar Afghanistan, tare da yi masa maraba da zuwa a nan kasar Sin, wanda ya kasance ziyararsa ta farko bayan zamansa shugaban kasar, kuma da halartar bikin bude taron ministocin harkokin waje da zai yi a nan birnin Beijing kan batun Afghanistan.

Yayin ganawar, Mr Xi ya nuna cewa, Sin tana goyon bayan Afghanistan da ta kiyaye 'yancin kanta da ikon mulkinta da cikakken yankinta, sannan tana nuna goyon baya ga tsarin shimfida zaman lafiyar da kasar ke dauka baya mai jigon "Bar jama'ar Afghanistan su gudanar da harkokin kasarsu", yana sa ran ganin kasar Afghanistan mai hadin gwiwa, mai karko da ta samu bunkasuwa da sada zumunci da sauran kasashe.

Ban da haka kuma, Mr Xi ya nanata cewa, Sin za ta karbi bakuncin taron ministoci karo na hudu kan yunkurin samun zaman lafiya na Istambul, wanda zai kasance karo na farko da aka yi kan batun Afghanistan bayan kafuwar sabuwar gwamnatin kasar, don haka Sin na fatan kara hadin gwiwa da Afghanistan don sa kaimi ga samun ci gaba a taron tare da kokarin samun goyon baya daga kasa da kasa da shiyya-shiyya da kuma al'ummar duniya kan Afghanistan.

A nashi bangare kuwa, Shugaba Ashraf Ghani Ahmadzai ya ce, jama'arsa na sa ran samun zaman lafiya, karko da bunkasuwa cikin sauri, yana kuma godiya sosai kan taimakon da Sin ke baiwa kasar wajen shimfida zaman lafiya da farfado da ita. Ya ce Sin sahihiyar abokiyar kasar ce, a don haka yana yabawa kan bunkasuwa mai karko da Sin ke samu, kuma ya yi imani da cewa, Afghanistan za ta samu bunkasuwa mai sauri bisa ga taimakon kasar Sin.

Kazalika, kasar na fatan zurfafa dangantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu bisa manyan ka'idoji biyar na zaman tare cikin lumana. Daga nan sai ya gode bisa ga gudunmawar da Sin ta bayar wajen shirya taron ministocin harkokin waje a wannan karo, da kuma fatan Sin zata ci gaba da ba da gudunmawa kan batun Afghanistan. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China