A yau Laraba 15 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron yin shawarwari kan aikin nuna fasahohi a nan birnin Beijing, inda ya jaddada cewa, dole ne masu aikin nuna fasahohi su ba jama'a a muhimmin matsayi a yayin da suke samar da sabbin ayyukansu, a kokarin samar da mafi yawan ayyuka masu kyau.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, yayin da rayuwar jama'a ke samun kyautatuwa a kai a kai, bukatun jama'a kan ingancin shirye-shiryen nuna fasahohi sun karu sosai don haka kamata ya yi sassa daban daban su kokarta biya bukatun jama'a a fannoni daban daban yadda ya kamata.(Fatima)