Da farko dai, shugaba Xi ya yi maraba da ziyarar da shugaba Jakaya Kikwete ya kawo nan kasar Sin a yayin da ake murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Tanzania. Shugaba Xi ya ce, ya kamata kasashen biyu su kasance abin koyi kan yadda suke tinkarar matsaloli iri daban daban cikin hadin gwiwa a ko da yaushe. Sannan ya kamata kasashen biyu su kasance abin koyi wajen yin hadin gwiwa domin neman moriya da samun nasara tare. Haka kuma, ya kamata, kasashen biyu su kasance tamkar abin koyi wajen neman cigaba tare a dukkan fannoni. Bugu da kari, shugaba Xi Jinping yana fatan kasashen biyu za su kasance abin koyi wajen shimfida zaman lafiya a duniya da kare moriyarsu tare, kamar a fannonin daidaita harkokin MDD, da tinkarar sauyin yanayin duniya da sauran batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya. (Sanusi Chen)