in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ganawa tsakanin Xi Jinping da Obama za ta kara inganta sabuwar dangantakar dake tsakanin manyan kasashen duniya
2014-10-20 14:57:45 cri
A ranar 19 ga wata a birnin Washington na Amurka, jakadan Sin dake kasar Amurka Cui Tiankai ya bayyana game da ganawa a tsakanin shugaban Sin Xi Jinping da takwaran aikinsa na kasar Amurka Barack Obama da za a yi a wata mai zuwa a nan birnin Beijing cewa, burin wannan ganawa shi ne na kara sa kaimi ga inganta sabuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka. Shugabannin kasashen biyu za su yi ganawa tare da yin shawarwari, ta haka ne za su tsara manufofi da hanyoyi kan yadda za a inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma wadannan manufofin da za su tsara suna da muhimmanci ga hadin gwiwarsu a fannoni daban daban.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama zai kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin domin halartar kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC a wata mai zuwa, kana zai gana da shugaban kasar Sin Xi Jinping. Cui Tiankai ya bayyana cewa, ganawar za ta kara sa kaimi ga inganta sabuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, kuma don cimma wannan buri, kamata ya yi Sin da Amurka su tattauna tare da yin hadin gwiwa kan manyan batutuwan da suka shafi duniya da shiyya-shiyya, har ma batutuwan da suka shafi kasashen biyu, wadanda suka hada da sauyawar yanayi, cutar Ebola, yaki da ta'addanci, hana yaduwar manyan makaman kare-dangi, makamashi mai tsabta, makamashin da za a iya sake yin amfani da shi, yarjejeniyar zuba jari a tsakanin kasashen biyu da dai sauransu.

Game da ci gaban da aka samu bayan da kasashen Sin da Amurka suka sanar da kafa sabuwar dangantaka a tsakanin manyan kasashe a shekara fiye da daya da suka wuce, Cui Tiankai ya bayyana cewa, hakika dai an samu ci gaba kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ko da kasancewar wasu matsaloli da sabane-sabane a tsakaninsu, amma abin farin ciki shi ne, an ga yadda kasashen biyu suke kokarin daidaita matsalolin da kawar da bambance-bambance dake tsakaninsu bisa tushen kara fahimtar juna da amincewar juna. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China