Mr. Xi ya kara da cewa, tun lokacin da aka fara gudanar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, Sin ta samu ci gaba mai kyau wajen taimakawa talakawa, hakan ya taimaka ga aikin kawar talauci a duniya baki daya.
Ban da haka kuma, Mr. Xi ya nanata cewa, bangare da ya fi kawo kalubale wajen tabbatar da zaman al'umma mai wadata shi ne kula da wasu yankuna dake fama da talauci a ganin shi ya kamata, jam'iyya da dukkanin al'umma su hada kai ta fuskar kawar da talauci.
Sai kuma a nasa bangaren, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ba da umurnin cewa, ana fuskantar hali mai tsanani wajen kawar da talauci yanzu, ya kamata a dauki matakai da suka dace domin aiwatar da wannan aiki, da suka hada da zurfafa yin kwaskwarima, kyautata manufofi, kara samun ci gaba a wasu wurare dake fama da talauci da sauransu.
Bugu da kari, a gun taron, an baiwa daidaikun mutane da wasu kungiyoyi lambobin yabo kan aikin kawar da talauci. (Amina)