Ministan ya ce, yankunan tsakiya da kudancin Asiya muhimman sassa ne na nahiyar Asiya da Turai. Kasashen hudu da shugaban kasar Sin ya ziyarta a wannan karo dukkansu muhimman kasashe ne da hanyar siliki ta ratsa a zamanin da, wadanda kuma suka fara cudanya tare da kasar Sin tun lokacin da. Kasashen sun kasance muhimman madogarai wajen bunkasa yankin tattalin arziki da hanyar siliki ta ratsa da kuma hanyar siliki ta kan teku cikin karni na 21. Shugaban kasar Sin ya kai wannan ziyara ce bisa yin la'akari da halin da ake ciki a gida da kuma waje. Manufar bunkasa yankin tattalin arziki da hanyar siliki ta ratsa da kuma hanyar siliki ta kan teku cikin karni na 21 ita ce hada kan al'ummar kasashen da zummar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaban sassan.(Lubabatu)