A yau Jumma'a ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Tanzaniya Jakaya Mrisho Kikwete a nan Beijing, inda ya sanar da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ba wa kasashen yammacin Afirka tallafi zagaye na hudu don yaki da annobar cutar Ebola.
Shugaba Xi ya nuna cewa, yanzu kasashen yammacin Afirka na kokarin hana yaduwar annobar cutar ta Ebola, wadda take yin barazana ga tsaron lafiyar jama'ar Afirka, bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma a nahiyar Afirka da kuma tsaron lafiyar al'ummar duniya.
A kokarin biyan bukatun kasashen da ke fama da annobar da kuma hana yaduwarta, gwamnatin Sin za ta kaddamar da wani shirin tallafi zagaye na hudu, inda za ta baiwa kasashen Liberia, Saliyo da Guinea da kungiyoyin kasa da kasa masu ruwa da tsaki kayayyaki da kudade wadanda darajarsu za ta kai kudin Sin yuan miliyan dari 5, tare da kara tura masana masu ilmin yaki da annoba da kuma ma'aikatan kiwon lafiya, sa'an nan kasar Sin za ta taimaka wa Liberia wajen gina wata cibiyar ba da jinya. Har wa yau kasar Sin na son yin hadin gwiwa da kasashen duniya cikin himma wajen taimakawa kasashen da ke fama da annobar ta yadda za su samu nasarar yaki da annobar cikin hanzari. (Tasallah)