in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya karbi takardun aiki na sabbin jakadun kasashe 9 da ke nan kasar Sin
2014-10-16 15:30:31 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya karbi takardun aiki na sabbin jakadun kasashe 9 da ke nan kasar Sin a jiya Laraba 15 ga wata a babban dakin taron jama'ar kasar Sin, wadanda suka zo daga kasashen Nijar, Liberia, Guinea, Cote d'Ivoire, Chile, Faransa, Iran, Peru da kuma kungiyar tarayyar Turai.

Xi Jinping ya yi marhabin da zuwansu kasar Sin don kaddamar da aikin wakilcin kasashen a nan kasar Sin, tare da jaddada cewa, kasar Sin na dukufa kan kiyaye zaman lafiya a duniya, kara azama ga samun bunkasuwa gaba daya. Haka kuma kasar Sin na da aniyar kara inganta cudanyarta tare da kasa da kasa don yin amfani da kyawawan zarafofi da tinkarar kalubaloli tare, a kokarin yin hadin gwiwa don samun nasara tare.

Haka zakila, Xi ya yi nuni da cewa, yanzu cutar Ebola mai saurin kisa na yaduwa a yammacin Afirka, wadda ke cigaba da kawo babbar barazana ga rayuka da lafiyar jama'ar wannan shiyya. Cutar Ebola ta zama kalubale da ke gaban dukkan kasashen duniya. Kasar Sin, a cewar shugaba Xi Jinping ta samar da taimako da goyon baya ga kasashen da ke fama da cutar, a kokarin ba su kwarin gwiwa don yaki da cutar tare da sauran kasashe.

A nasu bangare, sabbin jakadun sun bayyana cewa, ci gaban kasar Sin wata muhimmiyar dama ce ga duniya baki daya, kasashe daban daban na dora muhimmanci sosai kan dangantaka a tsakaninsu da kasar Sin. Za su yi namijin kokarinsu wajen inganta hadin gwiwa da cudanyar al'adu tsakanin kasashensu da kasar Sin, tare kuma da tinkarar kalubaloli daban daban na duniya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China