Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon jaje ga takwaransa na Nigreria Goodluck Jonathan da kuma shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma, a sakamakon rushewar wani ginin coci a birnin Ikko, hedkwatar kasuwancin kasar.
Rushewar ginin ta yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 115, wadanda suka hada har da mutane 84, 'yan asalin kasar Afrika ta Kudu, an ba da tabbacin cewar, lallai sun mutu a yayin hadarin da ya faru a ranar 12 ga wannan wata.
Shugaban kasar ta Sin ya ce, a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, yana mika cikakkiyar gaisuwa da jaje ga iyalan wadanda suka rasu da kuma wadanda suka sami rauni a sakamakon rushewar ginin, wadda ta haifar da salwantar rayuwar jama'a. (Suwaiba)