Ranar 30 ga watan Satumba rana ce ta farko ta tunawa da mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu domin kasar Sin da jama'arta, kuma wannan rana ta kasance jajibirin ranar cika shekaru 65 da kafa sabuwar kasar Sin. A wannan rana da safe, shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da mahukuntan kasar ciki har da shugaban kasar Xi Jinping, firaministan kasar Li Keqiang da sauran manyan shugabanni sun hallara a dandalin Tian'anmen dake nan birnin Beijing, inda suka aza kambun furani ga tubalin jaruman kasa tare da wakilai daga bangarori daban daban na birnin Beijing don tunawa da jaruman kasar.
Bikin aza furannin ga tubalin jaruman kasa don nuna alhini ga jaruman kasar wani muhimmin aiki ne da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasa suka saba yi tun shekaru da dama da suka gabata.
A ranar 31 ga watan Agusta na bana, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya zartas da kudurin ayyana ranar 30 ga watan Satumban ko wace shekara a matsayin ranar tunawa da mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu domin kasar Sin da jama'arta bisa doka, inda aka amince a rika gudanar da bikin tunawa da wadannan jaruwai a wannan rana a kowace shekara.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, mutane kimanin dubu 2 ne suka mutu a kokarin neman 'yantar da kasar Sin da jama'arta, da raya kasa, da kuma kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar. Yayin tunawa da wannan ranar a karo na farko, za a gudanar da bukukuwan a wuraren daban daban na kasar Sin da wasu ofisoshin jakadancin Sin da ke kasashen waje. (Zainab)