in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Indiya sun dauki niyyar kara zurfafa dangantakar kasashensu
2014-09-19 10:20:06 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana a ranar Alhamis a birnin New Delhi da takwaransa na kasar Indiya Pranab Mukherjee, inda suka dauki niyyar kara zurfafa dangantaka da karfafa wata manufar yarda da juna ta musammun tsakanin manyan kasashen biyu dake shiyyar Asiya.

Mista Xi da ya isa ranar Laraba a kasar Indiya a wata ziyarar aiki a cikin wannan kasa, ya bayyana a yayin wannan ganawa cewa, kasar Sin da kasar Indiya, dukkansu kasashe ne da tattalin arzikinsu ke tasowa, kuma sun kasance wani karfi mai tasiri ga wannan duniya. Ci gaban dangantaka tsakanin kasashen biyu bai tsaya kawai ga huldar abokantaka ba, har ya zama wani muhimmin fatan alheri ga shiyyar Asiya da duniya baki daya, in ji Xi. Shugaban kasar Sin ya nuna cewa, ya kamata kasashen biyu su ci gaba da zurfafa manufar yarda da juna ta musammun, da karfafa sahihiyyar dangantaka da bunkasa abokantaka tsakanin al'ummomin biyu, tare da kokarin warware sabanin dake tsakanin kasashen biyu cikin daidaici, ta yadda za'a iyar bunkasa dangantaka mai kyau da kasancewa bisa hanya mai kyau. Mista Mukherjee ya yaba da sakamakon da aka samu mai kyau na taron da aka yi a rana guda tsakanin mista Xi da faraministan kasar Indiya Narendra Modi, musammun ma kan yarjejeniyoyin da bangarorin biyu suka rattabawa hannu.

A cewar mista Mukherjee, bangaren kasar Indiya na amincewa da kara zurfafa dangantaka tare da kasar Sin, girmama moriyar juna da batutuwan dake janyo hankalin juna, da kuma warware bisa tunani mai zurfi wasu batutuwan dake kan tebur. Haka kuma shugaban Indiya ya ce, ana maraba da zuba jarin kasar Sin a fannin fasahohin zamani na sadarwa, bangaren masana'antu, da kuma gine-gine kamar gina layin dogo, hanyoyi da gadoji a kasar Indiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China