Kafofin watsa labaru na kasar Turkiya sun ba da labari cewa, a 'yan kwanakin nan, kurdawa dake Turkiya suna ta tsallaka zuwa yankin Syria, inda suka shiga yakin da ake yi tare da dakarun ISIS masu kaifin kishin Islama. Haka zalika, wasu Kurdawa kimanin dubu 150 wadanda da ma suke zaune a kasar Syria sun yi gudun hijira zuwa kasar Turkiya.
A nata bangare, gwamnatin kasar Turkiya ta rufe yawancin iyakokinta da Syria don hana Kurdawan kasar shiga cikin yakin dake kewayen kasar Syria. Hakan ya kara jinkiri ga hukumar Turkiya kan yanke shawarar shiga cikin kawancen da aka kafa don dakile dakaru masu tsattsauran ra'ayi, abin da ya sa Kurdawa na kasar Turkiya suka nuna rashin gamsuwa ga gwamnatin kasarsu sosai. Saboda haka, a kwanakin baya, suka yi dauki-ba-dadi da sojojin kasar wadanda aka girke a kan iyakar kasar, inda Kurdawa suka rika jifan sojojin da duwatsu, yayin da sojoji suka mayar da martani ta hanyar harba musu barkonon tsohuwa. (Bello Wang)