Kwamitin sulhun ya fada a cikin wata sanarwa cewar wannan laifin da aka tabuka wani abun tausayi ne dake tunatar da jama'a Karin barazana da masu gudanar da ayyukan agajin ke kara fuskanta daga kungiyar ta ISIS , kisan kuma manuniya ce a game da ayyukan zalunci da ake yiwa jama'ar Syria da Iraqi.
Kungiyar ta ISIS, tuni ta yi shelar ita ke da alhakin kisan ma'aikacin agajin wanda take tsare dashi tun a shekarar ta 2013, a lokacin yana ma'aikacin agaji na kasar Syria.
Kawo ya zuwa yanzu kungiyar mai tsattsauran ra'ayi ta hallaka 'yan jaraida guda biyu, James Foley da Steven Sotloff da kuma ma'aikacin agaji na Britania David Haines, dukkanin su wadanda aka yiwa yankan wuka, sannan kuma aka nuna mummunan kisan kan a cikin wani bidiyo.
Kwamitin sulhun MDD, ya ce dole ne a murkushe 'yan kungiyar Islamar ta ISIS tare da karya lagon rashin kauna a tsakanin jama'a(Suwaiba)