A wannan rana, shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, farmaki ta sama da kasar Amurka da kawayenta suka kai wa ISIS ba su iya kawar da kungiyar kwata-kwata ba. Saboda haka, kamata ya yi kasashen duniya su kara daukar matakan da suka dace, wato ba kawai a kai farmaki ta sama ba, har ma za a kaddamar da hari ta kasa. Shugaban ya kara da cewa, kasarsa za ta yi iyakacin kokarinta da nufin yaki da dukkan kungiyoyin ta'addanci na yankin.
A nasa bangaren ma, shugaba Barack Obama na kasar Amurka a cikin wata hira da aka watsa a tashar CBS a daren ranar 28 ga watan nan, ya amince da cewa, hukumomin leken asiri na kasarsa ba su zaci cewa, ISIS tana da karfi kamar haka ba, a waje guda kuma sun auna karfin sojojin Iraki fiye da kima. Sakamakon kuskuren hasashen da Amurka ta yi ne, yankin Gabas ta Tsakiya ya kasance masomin ISIS. A cewar Obama, daga karshe dai dole ne a warware rikicin Iraki da Syria a siyasance. (Bilkisu)