in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya yi kira da a taimakawa jama'ar Syria wajen yaki da dakarun ISIS
2014-10-08 13:25:16 cri
Staffan de Mistura, manzon musamman na babban magatakardan MDD kan batun Syria, a ranar 7 ga wata a birnin Geneva na kasar Switzerland ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su dauki matakan tallafawa jama'ar garin Kobane na kasar Syria, kan kokarin su na kare kai daga harin da dakarun ISIS ke yi musu.

Cikin bayanin sa, mista Mistura ya ce dakarun kungiyar ISIS masu kaifin kishin Islama suna ta kokarin mamaye karin garuruwa a kasashen Iraki da Syria, yunkurin da ya yi sanadin ta'asa a kasashen 2. Yanzu a kasar Syria, an riga an yi makwanni 3 ana yin kawanya ga jama'a kimanin dubu 400 na garin Kobane dake arewacin kasar wanda ke kan iyakar kasar da Turkiya, don haka ana bukatar samun taimakon gaggawa daga gamayyar kasa da kasa, in ji mista Mistura.

Sai dai a cewar jami'in, kasar Turkiya dake dab da garin ta riga ta karbi masu gudun hijira kimanin dubu 200 na garin Kobane, sa'an nan ya yi gargadin cewa kar a nade hannu a bar garin Kobane ya fada a hannun kungiyar ISIS.

Duk a ranar Talata har ila yau, shugaban kasar Turkiya, Recep Erdogan, ya yi kira ga kasashen yammacin duniya da su tura sojojin kasa domin kai hari ga dakarun kungiyar ISIS.

Sai dai a nata bangare, gwamnatin kasar Iraki ta sanar a ranar Talata nan 7 ga wata cewa, ba ta amince da duk wata kasa da ta tura sojoji cikin kasar ta a yunkurin dakile dakaru ISIS ba tare da samun amincewa daga gwamnatinta ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China