Wata jaridar kasar da ake kira "the star," ta ce hukumomin Malaysia sun kai samame a kan wasu rukunonin gidaje 2 dake Taman Bulkit, Jalil a kuala Lumpur, a ranar laraba a inda a lokacin ne suka gano bakin hauren wadanda suka shiga kasar ta Malaysia ba bisa ka'ida ba.
A yanzu dai ana yi wa su wadannan mutane baki da aka tsare tambayoyi,wadanda suka hada da yara 32 da manya 65 da kuma wani rukunin mutane mai yara 42 daga cikin adadin mutane 90.
Kasar Malaysia dai ta kara tsaurara matakan tsaro a kasar ta, a sakamakon wani rahoton jaridar kasar Indonesia, wanda yayi zargin cewar wasu matasa 4 'yan kabilar Uygur daga kasar Sin ,wadanda ake yiwa zargi da alaka da kungiyar Islama ta IS sun tsallaka ta Malaysia, suka shiga Indonesia inda nan take aka kama su, wannan yasa aka dauki matakin bincike a cibiyoyin dakatar da motoci na kan hanya.(Suwaiba)