A cewarsa, hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta sami wasu abubuwan dake cikin bayyanai daga mambobin ISIS da aka tsare.
Jami'in mai kula da aikin yaki da ta'adanci na ofishin 'yan sandan birnin New York John Miller ya sanar da yin bincike kan lamarin bayan da ya samu gargadin da Al-Adad ya bayar.
A nata bangare kuma, fadar shugaban kasar Faransa ta ba da sanarwa a ran 25 ga wata cewa, shugaban kasar François Hollande ya halarci taron tsaron kasar da aka yi a wannan rana, inda ya yanke shawarar kara daukar matakai a wasu wuraren jama'a na kasar domin tinkarar ayyukan ta'adda.
Ban da haka kuma, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani wanda ke halartar babban taron MDD ya bayyana a wannan rana na 25 ga wata cewa, dalilin tasowar kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi, ciki hadda ISIS shi ne, tsari na kuskure da kasashen yamma ke dauka a yankin gabas ta tsakiya da dai sauran yankuna, don haka ya kamata kasashen duniya su hada kai a tinkare su. Kuma ya kamata a gano a kuma kawar da tushensu. (Amina)