A yayin da Obama yake yin jawabi a gun babban taron MDD a wannan rana, ya bayyana cewa, kungiyar ISIS ta aikata manyan laifuffuka da dama a yankunan kasar Iraki da na Syria. Ya ce, kasar Amurka za ta murkushe wannan kungiya ta hanyar kafa kawancen yaki da ita.
Kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta jaddada a ranar 24 ga wata cewa, harin saman da kasar Amurka ta kai ga 'yan ta'addan a kasar Syria ba ya bisa doka, don haka ta yi kira ga kasa da kasa dake dauke nauyin kansu da su tsara manufofin yaki da ta'addanci tare.
Hukumar watsa labaru ta shugaban kasar Rasha ta bayar da sanarwa a ranar 23 ga wata, cewa shugaban kasar Vładimir Putin ya buga wayar tarho ga babban Magatakardar MDD Ban Ki-moon don tattauna kan batun yaki da kungiyar ta'addanci, inda ya jaddada cewa, bai kamata ba a kai harin sama ga kungiyar ISIS a kasar Syria ba tare da samun izni daga gwamnatin kasar Syria ba. (Zainab)