in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan 'yan gudun hijira na Sham da suka tsira zuwa Lebanon ya wuce miliyan guda
2014-05-05 10:03:25 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD wato UNHCR ta sanar da wani rahoto a ran 4 ga wata a birnin Beirut cewa, ya zuwa yanzu yawan 'yan gudun hijira na kasar Sham da suka tsira zuwa Lebanon ya kai miliyan 1 da dubu 44, wanda ya karu da dubu 10 bisa yawan adadin 'yan gudun hijirar na makon jiya.

A ranar 4 ga wata, an shirya taron ministocin harkokin wajen kasashen da ke karbar 'yan gudun hijira na Sham wato Jordan, da Turkiya, da Iraki, da Lebanon, da kuma Masar a wani sansanin 'yan gudun hijira na Zaatari da ke jihar Mafraq ta kasar Jordan, inda aka yi kira da a dauki matakai don tinkarar kalubale daga rikicin Sham. Ministan harkokin wajen Jordan Nasser Judeh ya karfafa a gun taron cewa, hanyar siyasa ce kawai za ta daidaita rikicin Sham, kuma ta haka ne za 'a dakile matsalar rashin tausayawa halin da jama'ar kasar ta Sham suka shiga. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China