in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya dawo nan Beijing
2014-10-18 16:54:27 cri

Firaministan kasar Sin Mr Li Keqiang ya kammala ziyararsa a kasashen Jamus, Rasha, Italiya da hedkwatar kungiyar hatsi da aikin noma FAO ta MDD a safiyar yau Asabar 18 ga wata, kuma ya dawo nan birnin Beijing bayan ya cimma nasarar jagorantar shawarwari tsakanin gwamnatocin Sin da Jamus karo na uku, da yin shawarwari tare da takwaransa na kasar Rasha karo na 19, kuma da halartar taron koli na nahiyoyin Asiya da Turai karo na 10 da aka yi a birnin Milan na kasar Italiya da sauran wasu ragowar ayyuka.

Yayin da ya bar kasar ta Italiya, manyan shugabannin gwamnatin Italiya, jakadan kasar Sin dake kasar Li Ruining sun yi masa ban kwana a filin saukar jiragen sama wannan kasa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China