in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya fara ziyarar aiki a kasar Rasha
2014-10-13 11:05:17 cri

Bisa gayyatar da takwaransa na kasar Rasha Dmitry Medvedev ya yi masa ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa birnin Moscow a ran 12 ga wata da yamma bisa agogon wurin, inda ya fara ziyararsa ta aiki a kasar Rasha, haka kuma zai halarci taron ganawa tsakanin firayin ministocin kasashen Sin da Rasha karo na 19.

A cikin wani jawabin da ya bayar, Li Keqiang ya ce, huldar hadin gwiwa irin ta abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake kasancewa tsakanin Sin da Rasha ta riga ta shiga wani sabon mataki. Yana fatan ziyararsa za ta bayar da karin gudummawa ga kokarin kara zurfafa zumuncin gargajiya da kara yin hadin gwiwa irin na a zo a gani, ta yadda za a iya kara ciyar da huldar dake tsakanin kasashen biyu.

A yayin wannan ziyara a Rasha, Li Keqiang zai gana da shugaba Vladimir Putin da shugabannin majalisun dokokin kasar Rasha, kuma zai yi shawarwari da takwaransa na kasar Rasha Dmitry Medvedev. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China