in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya fara ziyara a Jamus a hukunce
2014-10-10 10:24:22 cri

Bisa goron gayyatar firaministan kasar Jamus Angela Merkel, takwaransa na Sin Li Keqiang ya isa filin jirgin saman soja na Tegel dake birnin Berlin a yammacin jiya Alhamis 9 ga wata, domin fara ziyara a kasar a hukunce.

Firaminista Li bayan saukar sa a Berlin ya bayyana cewa, a watan Maris na bana, an tabbatar da sabon matsayi na bunkasa sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni tsakanin Sin da Jamus. Ya zuwa yanzu, manyan jami'an kasashen biyu sun yi mu'amala da juna sosai, kuma an karfafa hadin gwiwa tsakaninsu zuwa wani sabon mataki. Don haka yana sanya ran cewa, zai yi musayar ra'ayi da shugabannin Jamus kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da sauran batutuwan da suka fi jawo hankalinsu, da kara amincewa da juna, da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya da samar da sabbin kayayyaki cikin dogon lokaci, da sada zumunci tsakanin jama'arsu, a kokarin sa kaimi ga bunkasa kyakkyawar dangantaka tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

A yayin ziyarar tasa, Li Keqiang zai gana da shugaban Jamus Joachim Gauck, sannan zai jagoranci taron shawarwari tsakanin gwamnatocin Sin da Jamus karo na uku tare da takwaransa Angela Merkel, da halartar dandalin tattaunawar hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da fasahohi tsakanin Sin da Jamus, da taron koli na Hamburg na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Turai a inda zai gabatar da jawabi.

Manyan jami'an Jamus da jakadan Sin a Jamus Shi Mingde suka tarbi firaministan lokacin da ya sauka a filin jirgin saman.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China