in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da babban direktan FAO
2014-10-16 09:39:42 cri

A jiya Laraba 15 ga wata da safe ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da babban direktan hukumar abinci da aikin gona ta MDD wato FAO Jose Graziano da Silva a birnin Rome .

A yayin ganawar, Li Keqiang ya yabawa hukumar ta FAO bisa kokarinta na tabbatar da tsaron abinci a duniya, sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa a fannin aikin gona da kuma gudanar da aikin kawar da talauci a fadin duniya.

Li Keqiang ya yi nuni da cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma, kasar Sin ta riga ta daidaita matsalolin da suka shafi abinci da tufaffi, amma duk da haka akwai mutane fiye da miliyan 100 da ke fama da talauci a kasar.

Kasar Sin za ta yi namijin kokari wajen kawar da talauci sakamakon yunwa, da yin imani da daidaita matsalar abinci da mutane biliyan 1 da miliyan 300 ke fama da ita da kanta, wannan zai taimaka wajen tabbatar da tsaron hatsi a duniya. Kana kasar Sin za ta kara yin mu'amala da nuna goyon baya ga hukumar FAO, da kuma zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, da kuma tsakaninta da hukumar FAO da sauran kasashen duniya a fannin aikin gona.

A nasa bangare, Graziano ya bayyana cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron hatsi a duniya da kawar da yunwa, kuma tana daya daga cikin manyan abokan hadin gwiwa na hukumar FAO. Hukumar tana son kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin don sa kaimi ga kiyaye bunkasuwar kasuwar hatsi ta duniya, da inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, da kuma tabbatar da tsaron abinci a duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China