Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying ta sanar a yau Juma'a 3 ga wata cewa, firaministan kasar Sin Mr. Li Keqiang zai kai ziyarar aiki a kasar Jamus tare da jagorantar shawarwari tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Jamus karo na uku daga ran 9 zuwa 15 ga wata, daga baya kuma, zai kai ziyarar aiki a kasar Rasha tare da jagorantar ganawar tsakanin firaministocin kasashen Sin da Rasha karo na 19, sannan kuma zai kai ziyar a kasar Italiya, duk bisa gayyatar takwarorinsa na wadannan kasashe Angela Dorothea Merkel, Alexander Medvedev da Matteo Renzi.
Madam Hua ta ce, bisa gayyatar da Jose Graziano da Silva babban jami'in kungiya mai kula da harkokin abinci da aikin gona ta MDD wato FAO ya yi masa, Mr. Li zai ziyarci kungiyar a ran 15 ga wata. Kuma bisa gayyatar da shugaban kwamitin nahiyar Turai Herman Van Rompuy da Matteo Renzi, shugaban kwamitin kungiyar kawancen kasashen Turai Jose Manuel Durao Barroso suka yi masa, Mr. Li zai halarci taron kolin shugabannin nahiyar Asiya da Turai karo na 10 da ragowar ayyuka a birnin Milan na kasar Italiya daga ran 16 zuwa 17. (Amina)