Hong Lei ya yi bayani cewa, firaminsitan kasar Sin Li Keqiang ya fara ziyarar aiki a kasar Rasha tun daga ranar Litinin 13 ga wata, kuma ya hada kai da takwaransa na kasar Dmitry Medvedev don jagorantar ganawa tsakanin su karo na 19. Bayan ganawar, firaministocin biyu sun fitar da hadaddiyar sanarwa game da ganawar. Har ila yau a ranar Talatan nan 14 ga wata, Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Vladimir Putin.
Hong Lei ya nanata cewa, kasashen biyu sun yi hadin kai ne bisa tushen mutunta juna, wannan ba ma kawai ya kawo amfani ga jama'ar kasashen biyu ba, hatta ma zai sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa a duniya. (Amina)