A jiya da yamma ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron kolin kasashen Asiya da Turai karo na 10 a birnin Milan tare da yin jawabi.
A cikin jawabinsa, Li Keqiang ya gabatar da shawarwari uku kan yadda za a sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Asiya da Turai. Na farko shi ne tabbatar da zaman lafiya da na karko a kasashen Asiya da Turai tare. Na biyu shi ne sa kaimi ga yin mu'amala da zuba jari ga ciniki cikin 'yanci a tsakanin kasashen Asiya da Turai. Na uku kuma shi ne kara yin mu'amalar al'adu da inganta zamantakewar al'umma a kasashen Asiya da Turai gaba daya.
Ban da wannan kuma, Li Keqiang ya jaddada cewa, a matsayinta na wata kasa a duniya kuma ta babban yankin Asiya da Turai, kasar Sin tana yin kokari wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa a fadin duniya. Kasar Sin za ta ci gaba da bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da aiwatar da manufofin sada zumunta a tsakaninta da kasashen dake makwabtaka da ita. Kana tana fatan samun moriyar tattalin arziki tare da sauran kasashen Asiya dake makwabtaka da ita, da daukar nauyin tabbatar da zaman lafiya tare, don tabbatar da yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Asiya cikin lumana a nan gaba. (Zainab)