A yayin ganawar da su, Mr. Li ya bayyana cewa, yanzu Sin tana kokarin zurfafa yin kwaskwarima a kasa, da kara bude kofa ga kasashen waje sannan bunkasuwar kasar ta kawo babban zarafi da kasuwanni ga kasashen duniya. Yace don haka Kasar za ta tsaya tsayin daka kan hanyar neman samun bunkasuwa cikin lumana, da ba da gudummawa ga duniya, a kokarin sada zumunci da kasashe makwabta da tabbatar da zaman lafiya a duniya.
A nasu bangare, jakadun sun nuna godiya ga firaminista Li, kuma sun isar da sakonnin taya murnar shugabannin kasashensu ga al'ummar kasar Sin da shugabanninsu. Ban da haka, jakadun sun yaba matuka bisa ga kokarin da Sin take yi na tabbatar da zaman lafiya a duniya, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da tinkarar kalubale a duniya da sauransu. Daga nan sai suka jaddada cewa, kasashen duniya suna dora muhimmanci sosai kan bunkasa dangantaka tsakaninsu da Sin, da fatan za su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu yadda ya kamata.(Fatima)