Firaminista Li ya bayyana cewa, raya tattalin arziki na dogaro da karfi cikin dogon lokaci. Tun daga shekarar bana zuwa yanzu, Sin tana fama da raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki a cikin mawuyacin halin da ake ciki, amma ba tare da gamuwa da babbar matsala ba. Sin ta bunkasa tattalin arzikinta ta hanyar yin gyare-gyare da samar da sabbin kayayyaki.
Ban da haka, firaminista Li ya kara da cewa, a nan gaba, tattalin arzikin Sin zai ci gaba da bunkasa cikin sauri, tare da ba da gudummawa ga tattalin arzikin duniya. A sabili da haka, Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya. Hakan zai ba da agaji ga hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Turai a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da samun moriyar juna a fannin tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu, a kokarin samar da makoma mai kyau tsakaninsu yadda ya kamata.(Fatima)