in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi alkawarin kara ba da tallafin da ya kai dala miliyan 16 don yaki da Ebola
2014-10-17 09:57:33 cri

Kasar Sin ta yi alkawarin kara samar da tallafin da ya kai a kalla Yuan miliyan 100, kwatankwacin dala miliyan 16 don taimakawa kasashen Afirka yaki da cutar Ebola.

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ne ya bayyana hakan, yayin taron kolin kasashen Asiya da Turai (ASEM) karo na 10, inda ya ce, gwamnatin kasar Sin a shirye take ta hada kai da sauran kasashen duniya don ganin an yaki cutar Ebola da ta gallabi kasashen yammacin Afirka, wadda a halin yanzu take barazana ga lafiyar al'ummar duniya.

Mr. Li ya ce, wannan tallafin zai kunshi motocin daukar marasa lafiya 60, babura 100 da kuma dubban tan-tan na kayayyakin kiwon lafiya da na kariya, baya ga kwararru a fannin lafiya da gwamnatin za ta tura don horas da ma'aikatan lafiya 10,000 na kasashen Afirka.

Kafin wannan tallafi, a watan Afrilu ma kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka tallafin dala miliyan 38, kwatankwacin Yuan miliyan 234 don yaki da cututtuka.

Kimanin shugabannin kasashe 53 ne ke halartar taron kolin na ASEM, inda aka shigar da kasashen Croatia da Kazakhstan a matsayin sabbin mambobin kungiyar.

Ana sa ran Mr. Li zai ziyarci kasar Italiya, zangonsa na karshe na rangadin da yake a kasashe 3, inda ya zuwa yanzu ya ziyarci kasashen Jamus da Russia. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China