A ranar Alhamis din nan 9 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya tashi daga nan birnin Beijing zuwa kasashen Jamus, Rasha da Italiya a wani ziyarar aiki daga wannan rana zuwa 17 ga watan nan da muke ciki.
A lokacin ziyararsa a Jamus, ana sa ran zai jagoranci tattaunawa karo na uku tsakanin gwamntocin kasashen biyu, shi da shugaba Angela Merkel. A kasar Rasha kuma, zai halarci taro na a kai a kai karo na 19 tsakanin shi da takwaransa Dmitry Medvedev.
Bisa gayyatar Jose Graziano da Silva, babban darekta a ofishin samar da abinci da aikin gona na MDD wato FAO, firaminista Li zai ziyarci cibiyar ofishin a birnin Rome dake Italiya.
Har ila yau, firaministan na kasar Sin zai halarci taron shugabanni karo na 10 na Asiya da yankin Turai da shi ma za'a yi a Milan bisa gayyatar shugaban kungiyar tarayyar Turai Herman Van Rompuy, firaministan Italiya Matteo Renzi da kuma shugaban kwamitin tarayyar Turai Jos Manuel Barroso. (Fatimah)