A cikin jawabinsa, Li Keqiang ya nuna godiya ga kwamitin wasannin Olympics na duniya a madadin gwamnatin kasar Sin bisa ga goyon baya da gudummawar data baiwa gasar wasannin Olympics ta matasa a birnin Nanjing, sannan kuma ya taya 'yan wasa daga kasa da kasa murnar samun kyakkyawan sakamakon gasanni.
Haka nan kuma Li Keqiang ya yi nuni da cewa, gudanar da gasar wasannin Olympics ta matasa a birnin Nanjing cikin nasara zai kara inganta mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin matasan kasar Sin da na kasashen duniya, da kara fahimtar juna da sada zumunta a tsakanin jama'ar kasar ta kasa da kasa, da kuma sa kaimi ga samar da zaman lafiya mai dorewa da wadata a duniya. (Zainab)