A lokacin ganawar Li Keqiang ya taya Chui Sai On murnar sake zama gwamnan yankin Macau, ya kuma yaba ma mista Chui kan ayyukan da ya yi a matsayin gwamnan yankin a wa'adin aikinsa na baya. Li Keqiang ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 15 bayan dawowar yankin Macau cikin kasar Sin, an sami babbar nasara bisa bin akidar "kasa daya amma mai tsari biyu".
Ban da wannan kuma, Li Keqiang ya jaddada cewa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar "kasa daya amma mai tsari biyu", da kuma tsari na 'bar 'yan Macau su aiwatar da harkokin yankin da kansu', da ci gaba da bin manufar cin gashin kai da dokokin tushe na yankin. A cewar firaministan za a goyi bayan gwamnan yankin da gwamnatin yankin don su aiwatar da harkokinsu bisa doka, da sa kaimi ga yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin yankin da babban yankin kasar Sin, da kuma barin yankin da ya taka rawar musamman kan aikin samun bunkasuwar kasar Sin. (Zainab)