in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang: dole ne a tabbatar da aiwatar da matakan kyautata zaman rayuwar al'umma
2014-09-12 21:02:31 cri

Jiya 11 ga watan Satumba, Mr. Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya kai rangadin aiki a birnin Tianjin bayan ya halarci bikin kaddamar da taron Davos na lokacin zafi.

A yayin rangadin, Li Keqiang ya ce, akwai bukatar a hanzarta sassauta harkokin siyasa da rage iko daga hannun gwamnati, kuma a yayin da ake rage iko daga hannun gwamnati, dole ne a sa ido kan ayyukan gwamnati, wannan kyakkyawan mataki ne ga kokarin karkata yadda ake rarraba moriya a hanlin yanzu. Mr. Li ya jaddada cewa, dole ne jama'a su san yadda ake tafiyar da al'amura, kuma a hanzarta kafa dokoki, ta yadda za a iya toshe duk wasu kofofi na cin hanci.

A karshen bara, Li Keqiang ya taba kai ziyara wani yankin dake yammacin birnin Tianjin, inda jama'a suke fama da matsalar rashin wurin kwana. Mr. Li ya nemi a hanzarta gina gidajen kwana, kuma ya alkawarta cewa, zai dawo wurin bayan shekara guda. Sabo da haka, bayan watanni 9 da suka gabata, Li Keqiang ya sake ziyartar wurin, inda ya ga yadda aka riga aka gina rukunonin gidajen kwana guda 59, kuma jama'a za su iya samun sabbin gidajen kwana a shekara mai zuwa. Mr. Li ya nemi gwamnatin wurin da ta tabbatar da ingancin gidajen kwana, da kuma samar da makarantu da kyawawan hanyoyin mota da kasuwanni da sauran ababen hawa da jama'a suke bukata, ta yadda jama'a za su iya cimma burinsu na samun kyawawan gidajen kwana da wuri. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China