A yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta matasa ta hada da wasanni da al'adu da bada ilmi a gu daya, wadda ta samar da wani dandali na yin mu'amala da koyi da juna ga matasa daga kasashe daban daban, kuma ta gwada manufar wasannin Olympics ga fadin duniya wato kara sauri, tashi tsaye, da kara nuna karfi da kwarewa.
Firaminista Li Keqiang ya ce, ana samun babban ci gaba a sha'anin wasanni na kasar Sin a shekarun baya. Birnin Beijing da na Zhangjiakou sun zama wuraren yin takara na neman damar gudanar da wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022, kuma jama'ar kasar Sin suna da kwarewa da kuma karfin gwiwa na gudanar da wasannin yadda ya kamata.
A nasa bangare, Mr Thomas Bach ya lura cewa, kasar Sin ta gudanar da gasar wasannin Olympics ta matasa cikin nasara, abin da ya sa kwamitin wasannin Olympics na duniya ya yaba wa kasar Sin ganin yadda ta shirya tare da gudanar da gasar yadda ya kamata ba tare da barnatar da kudade masu yawa ba. Mr Bach daga nan yayi fatan kasar Sin za ta ci gaba da bada gudummawa kan sha'anin wasannin Olympics na duniya. (Zainab)