A cikin wasikar, Li Keqiang ya nuna cewa, a cikin shekaru 30 da kasar Sin ta shiga hukumar IAEA, bangarorin biyu sun yi hadin gwiwa da samun nasarori a fannonin bunkasa makamashin nukiliya, nazarin nukiliya, kiyaye tsaron nukiliya da dai sauransu.
Haka kuma Mr Li Keqiang ya bayyana cewa, yanzu gwamnatin kasar Sin tana kokarin raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, da inganta sha'anin samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da makamashin nukiliya bisa tushen tabbatar da tsaro, har ila yau kasar tana son yin kokari tare da hukumar IAEA da sauran kasashe membobin hukumar wajen kara yin hadin gwiwa da raya sha'anin yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana. (Zainab)