Cikin sharhin, Mr. Zhou ya kuma bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a karfafa fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare ta hanyoyi daban daban da za su dace da juna, kuma a warware sabanin dake kasashen biyu ta hanyar yin shawarwari a maimakon ta hanyar rikici, haka kuma, ma'anar mutunta juna ita ce, a girmama babbar moriyar juna da kuma manyan al'amuran dake janyo hankulan kasashen, sa'a nan kuma, shugaba Xi ya kara da cewa, dangane da matsayin da kasar Sin ke tsayawa, ya kamata a girmama tsarin zaman takewar al'ummar da kasar ta zaba da kuma mulkin kan kasar. Bugu da kari, cimma moriyar juna shi ne babban tushen gina sabuwar dangatakar manyan kasashe, ya kamata kasashen biyu su mai da hankali kan wannan batu yadda ya kamata. (Maryam)