Mr. Fang Fenghui ya isa kasar Amurka ce a ran 13 ga wata don yin ziyarar aiki a kasar, sa'an nan ya ziyarci hukumar tsaro ta Pentagon a ran 15 ga wata. Kuma a yayin taron manema labaran da ya yi tare da Mr. Dempsey, Mr. Fang ya bayyana cewa, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ta kai wani matsayi na musamman, ya kamata a inganta dangantakar sojojin kasashen biyu cikin zaman karko.
A nasa bangare kuma, Mr. Dempsey ya ce, an samu sakamako masu gamsarwa da dama a yayin shawarwarin nasu, musamman ma kan wasu muhimman batutuwa. Kasar Amurka na dukufa wajen gina dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, ta yadda zai taimaka wajen rage kalubalolin da abin ya shafa da kasashen biyu ke fuskanta da kuma kawar da rashin fahimtar juna dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)