in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da mai ba da taimako ga shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaro
2014-09-09 21:30:24 cri

Yau Talata 9 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da madam Susan Rice, mai ba da taimako ga shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaro.

A yayin ganawar, mista Wang ya ce, kasar Sin na sa muhimmanci kan halartar shugaba Barack Obama na Amurka kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar yin hadin gwiwa na yankin Asiya da tekun Pacific ta fuskar tattalin arziki da za a yi a watan Nuwamban bana, da kuma ziyarar da zai kawo nan kasar Sin. Kasar Sin tana son inganta tuntubar juna da yin hadin gwiwa da kasar Amurka wajen shirya wadannan ayyuka yadda ya kamata, a kokarin tabbatar da samun kyakkyawan sakamako a yayin ziyarar ta shugaba Obama, da kuma nuna wata kyakkyawar alama a bayyane da ke nuna cewa, kasashen Sin da Amurka suna hada kansu ba tare da rufa-rufe ba, hakan zai kara samar wa duniyarmu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A nata bangaren kuma, madam Rice ta ce, kasar Amurka ta sake nanata fatanta na ganin an farfado da kasar Sin mai kwanciyar hankali, zaman lafiya da wadata cikin dogon lokaci. Amurka na mara wa kasar Sin baya wajen sauke nauyi yadda ya kamata cikin al'amuran kasa da kasa. Amurka kuma tana son yin kokari tare da Sin wajen raya sabuwar dangantaka a tsakanin manyan kasashen biyu. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China