in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya gana da sakataren harkokin waje da ministan kudi na Amurka
2014-07-10 20:45:53 cri
A yau Alhamis 10 ga wata a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sakataren harkokin waje na Amurka, John Kerry, da ministan kudi kasar, Jacob Lew da sauran manyan jami'ai a wannan wata tawaga wadanda suke halartar taron shawarwari kan tsare-tsare da tattalin arziki na Sin da Amurka karo na shida da kuma shawarwari bisa matsayin koli kan mu'amalar al'adun bil'adam tsakanin Sin da Amurka karo na biyar.

A lokacin ganawar Shugaba Xi ya bayyana cewa, an sami babban ci gaba cikin wadannan shawarwari biyu, tare da gabatar da muhimman sakwannin kyautatawa da kuma bunkasa dangantaka tsakanin bangarorin biyu.

Mr Shugaba Xi ya lura da cewace, a cikin shekaru 35 bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka, dangantaka tsakanin su ta fuskanci da matsaloli da dama, tare da samunabun da ya sanya suka samu fasahohi masu daraja. Don haka inji shi Kamata kamata ya yi kasashen biyu su tsaya tsayin daka kan kafa wata sabuwar dangantakar manyan kasashe mara tashin hankali, da girmama juna, da samun moriya, a kokarin kara amincewa da juna, yta yadda za'a sa kaimi ga bunkasa dangantaka tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare, Jacob Lew ya bayyana cewa, shugaban Amurka Barack Obama ya yi marhabin da ganin cewa kasar Sin tana bunkasa mai yadda ya kamata lami lafiya don haka Amurka ba ta da niyyar hana bunkasuwar Sin, kuma ba ta son sabani ya shiga tsakanin su.

A wani bangaren kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin, Hong Lei a gun taron manema labaru da aka shirya a yau din nan, ya yi jawabi game da rana ta farko ta shawarwarin tsare-tsare da tattalin arziki na Sin da Amurka karo na shida ,inda ya ce abin mafi muhimmanci da aka gabatar a wannan rana shi ne, Sin da Amurka za su kafa wata sabuwar dangantakar manyan kasashen duniya ta hanyar yin hadin gwiwa tsakanin su.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China