in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya zanta da Barack Obama na Amurka
2014-07-15 15:07:34 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaran sa na kasar Amurka Barack Obama ta wayar tarho a jiya Talata, yayin da yake ci gaba da halartar taron BRICS a birnin Fortaleza na kasar Brazil.

Cikin tattaunawar tasu shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na maida hankali sosai ga dangantakar dake tsakaninta da kasar Amurka, tana kuma fatan dada kwazo tare da Amurkan, wajen karfafa dangantakar dake tsakaninsu. Xi ya ce nan gaba kamata ya yi kasashen biyu su cimma daidaito, ci gaba da kuma sa kaimi ga yin shawarwari kan yarjejeniyar zuba jari a tsakaninsu. A hannu guda kuma ya dace su kara yin hadin gwiwa, kan manyan batutuwan kasa da kasa, da na yankuna, ciki har da batun sauyin yanayi. Kana kasashen biyu su ci gaba da girmama juna, da warware matsalolinsu ta hanya mafi dacewa, da tabbatar da raya dangantakarsu yadda ya kamata.

Shi kuwa a nasa bangare shugaba Obama cewa ya yi, kasar Amurka na fatan hada kai da kasar Sin wajen kafa sabuwar dangantaka tsakanin manyan kasashen duniya, da kara yin hadin gwiwa, da maida hadin gwiwa a matsayin muhimman aiki yayin da ake raya dangantakarsu. Kaza lika kasar Amurka tana fatan kasashen biyu, za su ci gaba da yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da makamashi, da sauyin yanayi, da kuma manyan batutuwan kasa da kasa da na yankuna.

Bugu da kari shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan matsalar nukiliyar kasar Iran, inda shugaba Xi ya nuna cewa, an riga an samu ci gaba matuka wajen tattauna batun nukiliyar kasar ta Iran, koda yake dai ana fuskantar wasu wahalhalu. Ya ce kasar Sin na fatan bangarori daban daban da wannan batu ya shafa, za su yi iyakacin kokari wajen cimma matsaya a dukkan fannoni. Kana Sin na fatan kara kyautata mu'ammala da Amurka, a fagen cimma matsaya daya, da nufin daddale wata yarjejeniyar da za ta taimaka wajen warware matsalar nukiliyar kasar ta Iran cikin hanzari.

Shi kuwa shugaba Obama bayyana matsayin kasar Amurka ya yi game da wannan batu, yana mai jinjinawa kasar Sin game da muhimmiyar rawa da take takawa a batutuwan da suka shafi kasa da kasa, a lokaci daya kuma ya bayyana burin ci gaba da yin mu'amala da hadin gwiwa tare da kasar ta Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China