Dangane da furucin wani jami'in Amurka a zantawar sa da manema labaru kan dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika inda yace, bukatun samun makamashi daga Afrika da Sin take da shi ya canja burin kasar Sin wajen zuba jari a Afrika,kuma ya kamata Sin ta mai da hankali kan raya Afrika a dogon loakci, Madam Hua ta nuna cewa, Sin da Afrika sahihin abokan juna ne wajen yin hadin gwiwa.
Tace a matsayinsu na kasashe masu tasowa, Sin ta kan baiwa Afrika taimako gwargwadon karfinta bisa tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, tare kuma da kara hadin kai da kasashen Afrika domin kawo moriyar juna.
Madam Hua ya yi bayanin cewa Jarin da Sin take zubawa Afrika na taka rawa wajen kyautata halin bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar nahiyar, daga karfinsu na yin kirkire-kirkire, kyautata zaman rayuwar jama'a da kawar da taulaci. Har ila yau ta bayyana cewa manufar da Sin ta kan dauka kan Afrika na nacewa ga bayyana sahihanci da sada zumunci, nuna daidaici da adalci, kawo moriyar juna, samun bunkasuwa tare, matakin da ya zama babban dalilin da ya sa gwamnatocin kasashen Afrika da jama'arsu suke maraba da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika. (Amina)