in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban hafsan-hafsoshin sojan Sin ya gana da babban kwamandan sojin Amurka na hedkwatar Pacific
2014-07-09 11:00:34 cri
A jiya Talata ne mamba a kwamitin tsakiya mai kula da harkokin soja, kuma babban hafsan-hafsoshin sojan kasar Sin janar Fang Fenghui, ya gana da babban kwamandan sojin Amurka dake hedkwatar Pacific Samuel Locklear a nan birnin Beijing.

Shi dai Mr. Locklear ya zo birnin Beijing ne domin halartar taron shawarwari kan manyan tsare-tsare da batutuwan da suka shafi tattalin arzikin dake tsakanin kasashen Sin da Amurka zagaye na shida, da kuma taron shawarwari kan aikin tsaro bisa manyan tsare-tsare karo na hudu.

Yayin ganawar da suka yi Mr. Fang ya bayyana cewa, shugabannin kasashen biyu sun cimma matsayi guda kan gina sabuwar dangantakar manyan kasashe tsakaninsu, tare da bin wasu muhimman ka'idojin aiwatar da wannan aiki, lamarin dake da muhimmiyar ma'ana ga zaman lafiya da zaman karko tsakanin sojojin kasashen biyu da ma na yankin baki daya.

Janar Fang ya ce, cimma dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Amurka babban aiki ne, wanda ya kamata a kiyaye sakamakonsa yadda ya kamata, a kuma yi kokarin warware bambancin dake tsakanin kasashen biyu da nuna karfafa fahimtar juna, ta yadda za a iya ciyar da dangantakar abokantaka dake tsakaninsu gaba.

A nasa bangare, Mr. Locklear ya bayyana cewa, an samu muhimmin ci gaba wajen kyautata dangantakar kasashen biyu a fannonin tattaunawa da fahimtar juna, bisa kokarin da shugabannin kasahen biyu ke yi. Ya ce, a nan gaba ya kamata a mai da hankali kan bunkasuwar dangantakar kasashen biyu cikin dogon lokaci, a kuma warware bambancin ra'ayin dake tsakani hanyoyin da suka dace, ta yadda za a iya raya dangantakar kasashen da ta sojojinsu, bisa bukatun shugabannin kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China