in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya zanta da mai taimakawa shugaban kasar Amurka
2014-09-09 14:39:44 cri
Wakili a majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi ya tattauna da jami'a mai taimakawa shugaba Obama na Amurka ta fuskar harkokin tsaron kasar Susan Rice a Jiya Litinin.

Jami'an biyu dai sun zanta ne a babban masaukin baki na Diaoyutai dake nan birnin Beijing, inda kuma Mr.Yang ya shaidawa Rice cewa, a watan Yulin da ya gabata shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da shugaba Obama, kuma shugabannin biyu sun amince da kudurin ci gaba da raya sabuwar dangantakar dake tsakanin kasashensu.

Ya ce an samu muhimmin sakamako game da shawarwarin da suka yi ta fuskar tattalin arziki da manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu a zagaye na shida, da kuma tattaunawa tsakanin manyan jami'an kasashen biyu a fannin mu'amalar al'adu a zagaye na biyar.

Don haka Mr. Yang ya ce a nan gaba kamata ya yi kasashen biyu su aiwatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, a kuma karfafa fahimtar juna, da yin hadin gwiwa da mu'amala a fannoni daban daban, su kuma warware matsalolinsu yadda ya kamata.

Kaza lika Mr. Yang ya ce akwai bukatar tabbatar da kiyaye bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin yanayi na girmama juna, da hadin gwiwa, da samun moriyar juna yadda ya kamata.

A nata bangare madam Rice ta bayyana cewa, kasar Amurka na matukar mutunta dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana fatan za a ci gaba da yin shawarwari a tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, da tattauna kan batutuwan kasashen da suka shafi yankunansu, har ma da fadin duniya a dukkan fannoni.

Rice ta kara da cewa Amurka za ta ci gaba da kokari wajen kafa sabuwar dangantaka tsakanin ta da kasar Sin, wadda ta dace da moriyar kasashen biyu, ta kuma dace da huldodin kasa da kasa. Kana ta ce shugaba Obama ya na fatan ziyartar kasar Sin, domin halartar kwarya-kwaryan taron kungiyar APEC a watan Nuwambar dake tafe.

Har wa yau shugaban na Amurka ya yi imanin cewa, ziyarar ta sa za ta kasance mai muhimmanci a tarihin raya dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China