Mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang, da memban majalisar gudanarwar kasar Yang Jiechi wato su kasance tamkar wakilan musamman na shugaba Xi Jinping za su jagoranci shawarwarin tare da wakilan musamman na shugaban kasar Amurka Barack Obama wato sakataren harkokin waje na kasar John Kerry da kuma sakataren kudi na kasar Jacob Lew. Kuma mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong da Kerry za su jagoranci taron tattaunawar tare.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a gun shawarwarin, kasashen biyu za su yi musayar ra'ayoyi kan dangantakarsu, manufofin harkokin cikin gida da na waje, manyan batutuwan dake shafar su, ayyukan da kasashen biyu suka yi a yankin Asiya da tekun Pasific, manyan batutuwan kasa da kasa da yankuna da kuma kalubalen da ake fuskanta a duniya. Kana kasashen biyu za su yi shawarwari mai taken "inganta dangantakar abokantaka ta tattalin arziki mai girmama juna da samun moriyar juna", kuma za su yi taron musamman kan kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, zurfafa hadin gwiwar ciniki da zuba jari, bude kofa da yin kwaskwarima kan sha'anin hada-hadar kudi da kuma sa ido kan hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa. (Zainab)