in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna rashin jin dadinta game da rahoton harkokin sojan Sin da Amurka ta fitar
2014-06-07 16:38:35 cri
Game da rahoton harkokin soja da tsaron kasar Sin na shekarar 2014 da kasar Amurka ta fitar, kakakin ma'aikarar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yayin taron manema labaran da aka yi a nan birnin Beijing ranar Jumma'a 6 ga wata cewa, kasar Sin na tsaya tsayin daka wajen neman bunkasuwar kasa cikin zaman lafiya, kuma ita ce babbar kasa wadda ke dukufa wajen kiyaye zaman lafiya da zaman karko na yankin Asiya da Pacific, har ma da na kasa da kasa. Kasar Sin na bunkasa aikin sojojinta fuskar tsaron kasar don kiyaye 'yancin kai, mulkin kai da cikakken yankunan kasar, kuma wannan shi ne ikon ko wace kasa mai mulkin kai.

Ya kuma kara da cewa, kasar Sin ta amince da muhimmiyar ma'anar musayar ra'ayoyin dake tsakanin kasashen Sin da Amurka kan harkokin sojoji, kamar yadda rahoton ya bayyana, kuma kasar Sin na fatan Amurka ta kawar da bambancin ra'ayinta game da kasar Sin, domin ta gane ainihin ma'anar bunkasuwar harkokin sojojin kasar Sin yadda ya kamata, haka kuma ta kawar da zargi da gurguwar fahimtarta game da tsarin sojojin kasar Sin, dakatar da fitar da irin wannan rahoto, ta yadda za a iya inganta dangantakar sojojin kasashen biyu cikin zaman lafiya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China