Ranar 5 ga wata da safe bisa agogon birnin Washington, hedkwatar kasar Amurka, a cibiyar watsa labaru ta kasar Amurka an bude taron kara wa juna sani kan yadda kafofin yada labaru suke taka rawa wajen kyautata sabuwar hulda a tsakanin kasashen Sin da Amurka, wanda aka shirya domin kyautata mu'amalar da ke tsakanin kafofin yada labaru na Sin da Amurka da kuma kara samun fahimtar juna a tsakaninsu, a kokarin samar da kyakyyawan yanayi a zaman al'ummar kasa ta fuskar kyautata hulda a tsakanin kasashen 2.
A bikin bude taron, tsohon shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Cheng Siwei ya yi jawabi, inda ya ce, kafa sabuwar hulda a tsakanin kasashen Sin da Amurka, muhimmin ra'ayi daya ne da shugabannin kasashen 2 suka cimma, don haka ya kamata kafofin yada labaru na kasashen 2 su taka muhimmiyar rawa tare da sauke nauyi yadda ya kamata a wannan fanni. Ya kuma yi fatan cewa, kafofin yada labaru na kasashen 2 za su kulla zumunci a tsakaninsu ba tare da rufa-rufa ba, a kokarin kara ba da gudummowa wajen kyautata zumuncin da ke tsakanin jama'ar kasashen 2.
Xia Jixuan, mataimakin shugaban gidan rediyon kasar Sin CRI wanda yake daya daga cikin masu shirya taron shi ma ya ba da jawabi daga bisani kuma ya tattauna da takwarorinsa na Sin da Amurka. (Tasallah)