in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da takwaransa na Djibouti
2014-08-28 20:30:22 cri
A yau ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da takwaransa na kasar Djibouti Abdoulkader Kamil Mohamed a wajen bikin rufe gasar wasannin Olympics ta matasa a birnin Nanjing.

Yayin ganawar Li ya ce, Sin na da burin taimaka wa kokarin Djibouti na bunkasa tattalin arziki, samar da kayayyakin inganta rayuwar al'umma da samar da zaman lafiya a yankin.

Firaminista Li ya ce, Sin da Afirka manyan kasashe ne masu tasowa wadanda kuma ke da kasashe masu tasowa da dama a cikinsu, sannan suna da makoma da muradu iri daya baya ga kyakkyawar hadin gwiwar da ke tsakaninssu.

Don haka ya lashi takwabin inganta dangantakar moriyar juna dake tsakanin Sin da Afirka tare da kawo alheri da al'ummominsu.

A nasa jawabin Kamil Mohamed ya yaba da irin nasarorin da Sin ta samu tare da fatan koyan irin wadannan darussa daga Sin yayin da yake kara bunkasa dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu daga dukkan fannoni.

Ya ce Djibouti a shirye take ta yi amfani da yanayin da allah ya hore mata wajen kasancewar hanyar shigar da kayayyakin Sin zuwa Afirka. Ya kuma bayyana fatan kamfanonin Sin za su kara zuba jari a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China