A yayin ganawar, Li Keqiang ya nuna cewa, kasar Sin ta maida aikin samun ci gaba a matsayin aikin dake gaban kome, da kuma yin kokarin kyautata rayuwar jama'a da farko, sai dai ana bukatar yanayi na zaman lafiya a duniya yayin da ake kokarin samun bunkasuwa. Kana kasar Sin za ta ci gaba da bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, kuma tana son yin kokari tare da kasa da kasa ciki har da Jamus wajen kirkiro wata duniya mai zaman lafiya da wadata har abada.
A nata bangare, Merkel ta bayyana cewa, kasar Jamus tana son kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin, da kiyaye mu'amala tare da Sin kan harkokin kasa da kasa da yankuna, da sa kaimi da a inganta dangantakar kasashen biyu da kiyaye zaman lafiya da bunkasuwa tare. (Zainab)