Firaministan kasar Sin ya bayyana ra'ayin kasar Sin kan harkar teku a kasar Girka
Firaministan kasar Sin Li Keqiang wanda ke ziyara a kasar Girka dake nahiyar Turai ya yi wani jawabi a Jumma'a 20 ga wata, wajen wani taron da ya shafi yadda kasashen Sin da Girka za su iya hadin kansu a fannin harkar Teku a birnin Athens, fadar mulkin kasar, inda mista Li ya bayyana ra'ayin kasar Sin kan wannan batun, ya ce kasar Sin na son hadin gwiwa da sauran kasashen duniya, ta yadda za su iya yin amfani da teku don raya tattalin arzikin duniya, da karfafa hadin kai tsakanin kasa da kasa, don tabbatar da samun yankunan teku masu zaman lafiya da jituwa.
A Jumma'a wakilan gwamnatoci da kamfanonin kasashen Sin da Girka fiye da 300 suka halarci taron kan hadin gwiwar kasashen 2 a fannin harkar teku, inda jawabin firaministan kasar Sin ya zama daya daga cikin jawabai masu muhimmanci da aka bayar a wajen taron. A cewar mista Li, harkar teku na da muhimmanci ga zaman rayuwar dan Adam, sa'an nan kasashe da yawa na dogaro ne kan sarrafa albarkatun teku don neman ci gaban tattalin arzikinsu.
Firaministan ya ce ainihin abun dake cikin ra'ayin kasar Sin kan harkar teku shi ne kokarin tabbatar da zaman lafiya, hadin gwiwa, da jituwa. (Bello Wang)