Mr. Li ya bayyana hakan ne dai cikin jawabin da ya gabatar a jiya Asabar, yayin da yake halartar bikin bude sabon dakin adana kayayyakin tarihi na Herakleion dake kasar Girka.
Li wanda ya halarci taron tare da takwaransa na Girka Antonis Samaras ya kara da cewa, kasar Sin na fatan ci gaba da kokari tare da kasar Girka, wajen daukaka hadin gwiwar sassan biyu zuwa wani sabon matsayi, ta yadda hakan zai haifar da karin ci gaba a nahiyar Turai, da ma duniya baki daya.
A nasa bangare, Samaras cewa ya yi Sin da Girka na da dogon tarihi ta fuskar al'adu, wadanda suka hada sassan biyu waje guda. Ya ce Girka aminiyar kasar Sin ce ta dindindin. Kuma ziyarar aiki da firaminista Li ya gudanar a kasar ta samu babbar nasara.
Samaras ya kara da cewa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu na da muhimmanci kwarai ga Girka. Don haka kasar sa ke fatan zurfafa wannan dangantaka, a kokarin ta na samarwa al'ummun kasashen biyu alheri marsa iyaka.(Fatima)